December 27, 2024

Obi ya doke Tinubu a jihar Lagos – sakamakon wucin gadi

Lagos #Lagos

Sa’o’i 2 da suka wuce

Sakamakon wucin gadi da aka fitar a mataki na jiha ya nuna cewa dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar hamayya ta LP ya samu nasara zaɓen da aka gudanar a birnin ƙasar mafi girma, Legas.

Peter Obi na jam’iyyar Labour Party ya doke Bola Tinubu na jam’iyyar APC mai mulki a jihar Tinubun, kamar yadda sakamakon da hukumar zaɓe a jihar ta fitar ya nuna.

Wannan ne karon farko da jam’iyyar da Tinubu ke goyawa baya ta kasa lashe zaɓe a Legas tun bayan komawar ƙasar mulkin dimokraɗiyya a 1999.

Sai dai Tinubu ya samu nasara a jihohi uku cikin da aka bayyana sakamakonsu kawo yanzu – watau jihohin Kwara da Ekiti da kuma Ondo.

Amma jinkirin da ake samu wajen samun sakamakon zaɓen na sanya mutane cikin damuwa.

Hukumar zaɓen ƙasar ta nemi afuwa kan rashin sanya sakamakon zaɓe daga mazaɓu a shafinta na intanet, tana mai cewa an samu matsalar nau’rar ne saboda yawan mutanen da suke ƙoƙarin shiga domin samun bayanai.

A zaɓen shekarar 2019, Peter Obi ne ya yi wa Atiku Abubakar mataimaki a takarar shugaban ƙasa a ƙarkashin jam’iyyar PDP.

Leave a Reply