January 7, 2025

Mexico ta soma yiwa mutanen ta Allurar Korona

Mexique #Mexique

Wallafawa ranar: 24/12/2020 – 20:03

Kasar Mexique bayan samun kashi na farko na allurar rigakafin cutar Korona a ajiya laraba kamar yadda ministan kiwon lafiyan kasar Hugo Lopez Gateli ya sanar ta ayyana soma allurar rigakafin cutar Corona a yau alhamis.

Mexico ta sayo alluran ne daga hadin guiwar kamfanonin Pfizer da biotech,Mexico na cikin kasashen Duniya da cutar tafi barna.

Daga hukumomin kiwon lafiya alkaluma na bayanna cewa ya zuwa yanzu mutane dubu 120 suka hallaka a kasar sakamakon cutar ta korona, a kowacce rana sama da mutane dubu 10 ne ke kamuwa da cutar a wannan kasar ta Mexico.

Leave a Reply